1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaAustraliya

Muhawara kan bindigogi a Australiya

November 21, 2023

A Australiya ana kira bisa kwaskware dokokin da suka shafi mallakar bindigogi bayan kai hari kan wasu ‘yan sanda da ke bakin aiki. Tun shekarar 1996 aka saka dokar da ta haramta amfani da bindigogi masu sarrafa kansu.

https://p.dw.com/p/4ZGLy
'Yan sandan kasar Australiya a birnin Melbourne
'Yan sandan kasar AustraliyaHoto: Alexander Bogatyrev/SOPA Images/picture alliance/ZUMAPRESS

Sau biyu ke nan ake kiran ‘yan sanda zuwa wani wurin da ake fama da matsala dan su kawo dauki sai dai kafin su kai ga shawo kan lamarin aka halaka su da harbin bindiga. A kwanakin baya wani mutumi ne ke fada da matarsa aka je rabawa amma aka sami akasi ‘yan sandan da suka fara isa wurin ba su fita da rai ba. Ko da shi ke a wannan karon dan sanda daya ne ya mutu sauran sun yi munanar raunuka ne. Tim Quinn daga kungiyar "Gun Control" Australiya, kungiyar da ke da rajin kare yaduwar bindigogi ya ce yanzu da ake samun ci gaba a fasahohi da sabbin dabaru na zamani dokokin takaita yaduwar bindigogin ma na neman gyara.

Karin Bayani: Australiya ta kama gungun masu laifi

Mr Quinn ya yi bayanin haka ne domin a zahiri, kasashen duniya na yaba wa Australia saboda dokokin bindigoginta. Hasali ma tun wata kisar gillar da aka yi a shekarar 1996 ta sanya dokar da ta haramta bindigogi masu sarrafa kansu sa'annan ta gindaya wasu sharudda masu tsauri wa duk wanda ke so ya mallaki bindiga. Wadannan sharuddan sun hada da haramta amfani da bindigogi masu sarrafa kansu, tilasta rajistar bindigogin, da bayyana kwakwarar dalilin mallakar bindigar kafin mutun ya saya. Bacin haka kowace shekara ana bayar da damar maido bindigogin da mutun ya san bai kamata ya na da shi ba. Za'a iya yin hakan ba tar da biyan tara ko fuskantar wani hukunci ba.

Bindiga mai sarrafa kanta
Bindiga mai sarrafa kantaHoto: Hanna Sokolova/DW

To amma gibin da ake gani a dokar yanzu ya kasu gida biyu: Na farko dai yayin da aka haramtawa mutun mallakar bindiga bisa dalilan cewa zai kare kan shi, mutun na iya sayen bindigar idan har shi mamba ne na kungiyar masu sha'awar bindigogi kuma yanzu ana kiyasin cewa mambobin ire-iren wadannan kungiyoyin sun karu daga 30,000 a baya zuwa fiye da dubu 200 kuma rassan irin wadannan kungiyoyin a kasar yanzu sun fi 400. Inda ake kyautata zaton masu mugun nufi na iya fakewa da kungiyoyin.

Na biyu kuma shi ne kowace gwamnati na da na ta tsarin na sanya ido a kan wadanda suka mallaki bindiga saboda haka idan mai bindiga ya tashi daga jiharsa zai iya zuwa jihar da ba ta sa ba ya aikata ta'asa kamar yadda ya faru a daya daga cikin lokutan da ‘yan sandan suka halaka. Yayin da manyan jihohin kasar wato New South Wales da Queensland suka bayar da shawarar suka kuma ce a shirye su ke a hada rajistar kowace jiha saboda rundunonin kowace jiha su iya samun bayanan masu mallakar bindigogin kai tsaye, sauran kananan jihohin sun ce ba su da karfin yin hakan dan haka suna jiran gwamnatin tarayya a Canberra ta dafa musu amma har yanzu ba ta ce komai ba. Abun jira a gani dai shi ne ko gwamnati a Canberra za ta bayar da kudin da ake bukata ganin yadda al'umma ke matsin lamba. Karshen rahoton ke nan, Pinado Waba daga Australia.