1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta bude hanya ga bakin haure

Salissou Boukari AH
November 28, 2023

Shugaban Nijar Janar Abdoulrahamane Tiani ny dauki wani kudri inda ya soke dokar nan ta 2015 da gwamnatin ta Nijar ta dauka da ke haramta daukan bakin haure daga Agadez zuwa kan iyakar Nijar da Libiya ko Aljeriya.

https://p.dw.com/p/4ZX1Z
Hoto: Borja Suarez/REUTERS

 Dokar da shugaban kasa na mulkin soja ya dauka mai kudurori uku da ke dauke da sa hannun babban sakataran gwamnati Mahamane Roufai Laouali, a kudirinta na farko ta ce an soke wannan doka mai lamba 2015-36 ta ran 26 ga watan Mayu da ke haramta jigilar bakin haure, sannan kudiri na biyu na dokar ya ce duk hukuncin da aka dauka na dauri kan wannan doka duk an shafesu daga ranar da aka dauki  wannan kudiri.

Ba za a sake hukunta masu yunkurin ratsa hamadar Nijar ba da nufin zuwa Turai

Senegal | Schiffbruch vor der Küste Dakars
Hoto: Leo Correa/AP Photo/picture alliance

Sai dai kudiri na uku da ke cewa ba za a karbi duk wani batu na tambayar diyya ko wani makamanta haka da ka iya biyo bayan wannan mataki ba, inda aka ce ministan shari'a da kare hakin bil' Adama ya bi lamarin sau da kafa don ganin komai ya gudana yadda ake bukata. Sai dai daman kungiyoyi da dama masu kula da harkokin bakin haure sun yi ta kai ruwa rana na ganin an soke wannan doka,kuma a cewar  Hamidou Nabara na kungiyar JMED ci gaba ne a fannin mutunta 'yancin zirga-zirga.

Hadarin da ke tattare da ketare hamada domin zuwa Libiya da nufin zuwa Turai

Migranten auf den Kanaren
Hoto: Manuel Navarro/dpa/picture alliance

Wannan batu dai na bakin haure duk kuwa da yadda ake ganinshi a matsayin 'yancin na walwala ko   zirga-zirgar al'umma daga wannan kasa zuwa waccan, a hannun daya kuma lamari ne da ke tare da hadaruka inda aka sha samun gawawakin jama'a a dajin Sahara da wasu daga cikin masu jigilarsu ke yadasu wasu kuma ke bacewa a dokar daji. Lamarin da ake ganin dole sai an dauki mataki da zai kare hakkokin wadannan matafiya da yanzu suka samu izinin biyowa ta Nijar su fita ta inda suke so ba tare da hakan ya  zame babban laifi ba.