1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Kokarin magance matsalar karancin abinci

Uwais Abubakar Idris
October 6, 2023

Ma'aikatar kula da ayyukan gona da samar da wadatar abinci ta Najeriya ta sanar da sabbin dabarun magance karancin abinci da ke barazana ga jama'ar kasar

https://p.dw.com/p/4XDv8
Hoto: imago/Aurora Photos/Peter Essick

Jerin matakai daban daban ne dai ma'aikatar gonar da wadata abinci a Najeriyar ta zayyana domin shawo kan matsalar rashin wadatar abinci a kasar. Baya ga tsadar da kayan abinci ke yi, akwai kuma karancinsa, abinda ya Sanya sama da mutanen milyan 25 ke fuskantar barazanar yunwa a wannan shekarar. Minsitan ayyukan gona na Najeriyar Abubakar Kyari shine ya sanar da matakan.

Najeriya: Wata manomiya a cikin gona
Najeriya: Wata manomiya a cikin gonaHoto: Ifiok Ettang/AFP via Getty Images

Matakan sun hada da bunkasa noma da kiwo da samar da takin zamani da ingantaccen iri tare da maida hankali a kan mata da matasa da take son su rungumi noma a kasar. 

Najeriyar da ke fama da matsaloli na koma bayan aikin gona tana kuma fusknatar barazana ta sauyin yanayi, abinda Farfesa Mansur Bako Matazu darakta janar na hukumar kula da sauyin yanayi ta Najeriya ya bayyana abinda ya kamata a fahimta.

Najeriya: Kiwon dabbobi
Najeriya: Kiwon dabbobiHoto: Samson Adeleke/DW

Matsalar rashin tsaro da ta adabi manoman ta sa wurare da dama ba sa iya noma. Ministan gonar Abubakar Kyari yace akwai shiri da suka yi na tunkarar wannan matsalar.

Najeriyar dai na bukatar sauya tsarin yadda ake noma daga na gargajiya zuwa na zamani idan tana son ciyar da alummarta wacce aka yi kiyasin nan da shekara ta2050 za su kai milyan 400